Saturday, 7 July 2018

Buhari ya yaba wa juriyar Saraki a shari'arsa: Yace ya zama abin koyi ga 'Yan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani game da wanke shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da kotun koli ta yi.


Shugaban ya ce duk da kalubalen da bangaren shari'ar kasar ke fuskanta amma hakan ya nuna bangaren na aiki sosai, kuma babu wanda za a bari ya karya tsarin.

Shugaban ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu.

"Na ga shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki ya bi tafarki mafi wahala na bin matakan shari'a, ya jure, kuma daga karshe kotun koli ta ce ba ya da laifi" in ji shugaban.

Ya kara da cewa: "Akwai wasu lokutta da dama da wasu mutane cikin rashin tunani suke neman kawo lalaci ga bangaren shari'a duk don su kare kansu, maimakon mayar da hankali ga bin matakan da za su wanke kansu."

"Abinda na yi ke nan a zabuka uku da aka zalunce ni, kafin Allah ya ba ni damar tsayawa takara a karo na hudu." Buhari ya ce yadda Saraki ya dinga yawo tun daga karamar kotu zuwa kotu mafi girma a Najeriya ya zama babban misali da ya kamata dukkanin 'yan Najeriya su yi koyi da shi.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment