Sunday, 8 July 2018

Buhari Zai Aiwatar Da Sabon Karin Albashin Ma'aikata>>Oshiomhole

Sabon Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole ya tabbatar da cewa Shugaba Muhammad Buhari zai aiwatar da sabon karin albashi da zarar an cimma matsaya.


Oshiomhole ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da wakilan kungiyar Kwadago suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja inda ya ba su tabbacin zai zama idonsu wajen gwamnati ta mutunta hakkokin ma'aikata.
rariya

No comments:

Post a Comment