Thursday, 12 July 2018

Chelsea ta kori Antonio Conte daga aikin horar da 'yan kwallon ta

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kori me horas da 'yan wasanta, Antonio Conte, kocin yayi kakar wasa biyu a kungiyar inda a kakar wasan farko ya ciwa kungiyar kofin firimiya a ta biyu kuma ya ciwo kofin F.A.


Saidai an rika samun rashin jituwa tsakanin wasu daga cikin manyan masu gudanarwa na kungiyar da Conte wanda hakan ya fara alamta cewa da wuya ya dade a kungiyar.

A yau Alhamis, kafar watsa labarai ta Sky Italia ta ruwaito cewa kungiyar ta Chelsea ta gayawa Conte cewa an saukeshi daga mukaminshi.

No comments:

Post a Comment