Tuesday, 3 July 2018

Cristiano Ronaldo ya kulla yarjejeniya da Juventus zai buga musu kwallo har shekarar 2022

Sabbin rahotanni na bayyana cewa tauraron dan kwallon kafar Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Juventus zai buga musu kwallo har zuwa shekarar 2022 akan albashin Yuro miliyan talatin duk shekara.


Ronaldo dai na fada da kungiyarshi ta Real Madrid akan  karin albashi inda suka kasa cimma matsaya, abinda yasa yake neman barin kungiyar ruwa a jallo, ita kuma Juventus tayi amfani da wannan damar dan sayen dan wasan, kamar yanda Marca ta ruwaito.

Madrid dai na neman Yuro biliyan daya ne akan Ronaldo amma Juventus tayi imanin cewa za'a iya yin ciniki a samu ragi akan wannan kudi, bawai albashin da Juventus zata biya Ronaldo kawai bane yasa zai koma kungiyar, hadda girmamashi da tayi.

Duk da yana da shekaru 34 amma kungiyar a shirye take ta mayar dashi babban me ci mata kwallo ta hanyar sayar da Gonzalo Higuian, tabbas komawar Ronaldo Juventus daga Madrid ci bayane amma burinshi bazai wuce yaci kofin zakarun turai a kungiyoyi uku daban-daban ba.

No comments:

Post a Comment