Thursday, 12 July 2018

Croatia ta tsallaka wasan karshe a gasar kofin duniya: Ta kafa wani muhimmin tarihi

media
Kasar Croatia ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha bayan ta doke Ingila da kwallaye 2-1.

Yanzu haka Croatia wadda a karon farko kenan da take samun gurbi a wannan mataki, za ta kece raini da Faransa a wasan karshe a ranar Lahadi.
Kasashen biyu sun fara shafe tsawon mintina 90 suna kan kunnen doki 1-1, lamarin da ya sa aka kara musu lokaci, yayin da Croatia ta kara kwallo ta biyu ta hannun Mario Mandzukic.
Ingila ce ta fara zura kwallo a minti na 5 da saka wasan ta hannun Kieran Trippier, amma Ivan Perisic ya farke a minti na 68.
Tarihi ya nuna cewa, a can baya, kasashen biyu sun hadu sau daya a wata babbar gasa, in da Ingila ta samu nasara da ci 4-2 a matakin rukuni a shekarar 2004 a gasar cin kofin kasashen Turai.
Amma a jumulce, sun hadu sau takwas, in da Ingila ta samu nasara a wasanni hudu ,Croatia ta samu nasara a wasanni uku, sannan suka tashi canjarasa a wasa guda.
rfihausa.
Kasar ta Croatia na da jama'a da yawan su bai wuce miliyan hudu da dubu dari biyu ba.
Wannan yasa suka kafa tarihin kasancewa kasa mafi karancin yawan jama'a da suka kai wannan mataki tun daga shekarar 1930, shekaru tamanin da takwas kenan da suka gabata.
'Yan Najeriya da dama ne suka rika bayyana murnarsu da tsallewar Croatia zuwa wannan mataki, inda wasu ke cewa saboda mun fada rukuni daya dasu a gasar.

No comments:

Post a Comment