Tuesday, 31 July 2018

Daga share-share a filin jirgi ya zama babban matukin jirgin sama

Masu iya magana na cewa, me hakuri mawadacine, wataran zai dafa dutse, hakan ne ya faru da Muhammad Abubakar wanda shekaru 24 da suka gabata yake aikin goge jirgin sama amma yanzu ya kai matsayin Kyaftin a cikin matuka jirgin.


Kamfanin sufurin jiragen sama na Azman ne ya bayar da labarin Muhammad a dandalinshi na sada zumunta inda yace shekaru 24 da suka gabata Muhammad aikin goge jirgin sama yake amma yanzu ya zama matukin jirgi har ya kai matsayin Kyaftin, kamfanin ya tayashi murna.

Tun bayan wannan sanarwarce sai jama'a sukai ta taya Muhammad da addu'in fatan Alheri.


1 comment: