Tuesday, 10 July 2018

Dalibai sun kona makarantu saboda an hanasu satar jarabawa

Dalibai sun kona makarantu kwana guda bakwai a kasar Kenya a makon da ya gabata domin nuna adawa a kan wasu matakai masu tsauri da aka bullo da su domin hana satar amsa a lokacin jarrabawar da za su fara aiki a cikin watanni uku masu zuwa.

Ministar ilimin kasar Kenya Amina Muhammed ce ta bayyana hakan lokacin wani taron manema labarai.

Dalibai a wata makaranta sun nemi shugaban makarantarsu a kan ya yi mu su alkawarin cewa zai bar dalibai su yi satar amsa a lokacin jarrabawa, in ji ministar.

Wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta kasar ta fitar ta ce 'yan sanda sun kara kaimi wajen kawo karshen lamarin kuma an kama dalibai 125.

Kotu ta samu dalibai uku da laifi bayan da aka gurfanar da su a gabanta.

An kuma bayar da belin wasu dalibai biyar wadanda ake zarginsu da kona makarantar sakandare ta maza a garin Chulaimbo da ke Kisumu.

"An bukaci dukannin makarantu a kan su rubanya yawan malamai da ke bakin aiki nan da makoni biyu masu zuwa, tare da karfafa tsaro a makarantunkwana idan dalibai sun je aji karatu da daddare," in ji ma'aikatar ilimi.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment