Tuesday, 10 July 2018

Dan shekara biyu ya harbe kansa da bindiga


Wani yaro dan shekara biyu ya harbe kansa har lahira da wata bindiga da ya gani a cikin gidansu, kamar yadda hukumar 'yan sanda ta jihar Texas a Amurka ta rawaito.'Yan sanda sun ce iyayen yaron mai suna Christopher Williams Jr, na gida lokacin da yaron ya harbi kansa da bindigar a ka.

Kuma 'yan sandan na da yakinin cewa wata karamar bindiga da suka samu a wurin da al'amarin ya faru, mallakin mahaifin yaron ce.

Babu tabbaci ko za a gabatar da iyayen yaron a gaban shari'a bisa al'amarin.

Akwai yara da dama a Amurka da suka yi kuskuren harbin kansu da bindiga, abin da kan janyo su rasa ransu.

Jami'an tsaro na cewa suna son binciko yadda yaron ya kai ga bindigar, wadda ya yi amfani da ita wajen harbe kansa a ranar Lahadi da misalin karfe daya saura kwata na rana.

Hukumomi dai a kasar na ta kira ga iyaye da su rinka taka-tsan-tsan da bindigoginsu saboda guje wa irin haka.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment