Tuesday, 10 July 2018

Diyar shugaban kasa, Zahara Buhari ta haihu

Diyar shugaban kasa, Zahara Buhari wadda ke auren dan attajirin dan kasuwa, Ahmed Indimi ta haihu, Zahara Buhari ta haifi da Namiji kamar yanda rahotanni suka bayyana.Ma'aiakacin gidan rediyon muryar Amurka, Sale Shehu Ashaka ya ruwaito cewa Zaharar ta haifi da namiji a dandalinshi na sada zumunta.

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, Zaharar ko mijinta babu wanda ya bayyana komai a shafinshi na sada zumunta.

Saidai abinda zamuce shine Allah ya raya abinda ta haifa ya kuma basu lafiya ya kuma Albarkaci rayuwarshi.

No comments:

Post a Comment