Wednesday, 18 July 2018

Duk me bina saboda Buhari daga yau ya dena>>Nazir Ahmad Sarkin Waka

Tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad, Sarkin Waka, yayi suna wajan baiwa mutane hakuri akan lamurran dake faruwa musamman na harkar gwamnati, sau da dama idan ya wallafa hoto a dandalinshi na sada zumunta yakan rubuta cewa adai kara hakuri ko kuma a ci gaba da hakuri.


To da alamadai shima hakurin nashi ya kare, domin kuwa a wani sako da ya wallafa yace a gayawa APC cewa, an musu laifi, amma ba zasu bayyana lafin ba yanzu tukuna, irinshi matasan Arewa duk da gudummuwar da suka bayar amma anyi watsi dasu ba'a gode musu to zasu nuna cewa su haifaffune.

Bayan wallafa sakon sai ra'ayoyin jama'a ya fara kwarara inda wasu suka alakanta wannan magana da Nazir yayi da cewa, mukamin da aka baiwa Rarara ne ya mai zafi shi yasa yake wannan magana, wasu kuwa sun dauke ta da zafi inda suka rika mayarwa da Nazirdin kalamai, hadda zagi dake nuna cewa da Buhari yake kuma be kamata ya sa kanshi a siyasa ba.

Ga dai kadan daga cikin ra'ayoyin da wasu suka bayyana akan wannan sako:

Bayan wadannan ra'ayoyi da mutane suka bayyana, Nazir ya mayar da martani inda yace wai su dama haka suke?, shifa be kira sunan kowa ba yace dashi yake amma gashi sunzo sun zaginshi saboda Buhari.

Nazir ya bayar da misali da Bukhari wanda ya ruwaito hadisai daga manzon Allah(S.A.W) inda yace, shi kanshi malamai suna hada hadisinshi da ayar Qur'ani suce be ingantaba ballantana Buhari dake tare da Osinbajo ace ba za'a mai gayara ba idan yayi kuskure.

Ya kara da cewa, shin wai da mahafin masu zaginshi ya zaga yaya zasu yi kenan?, ga masu cewa Nazirun yana hassada ne saboda mukamin da aka baiwa Rarara, ya basu amsar cewa shi be ma san da wannan magana ba sai a bakinsu, kuma shi Allah ya tsareshi da yin hassada akan abinda zai kare a Duniya, yace, ga manyan mutane da zaiyi hassada akansu sai shi(Rarara)?, ya kara da cewa ko shekara dari zaiyi akan mukamin da aka bashi ba zai samu irin abinda gareshi ba.

Nazir ya kara da cewa kai duk me binshi a dandalinshi na sada zumunta saboda Buhari daga yau ya dena, sannan kuma zasu zaunama suyi shawara akan zamansu a cikin jam'iyyar tunda abin haka yake.

Ya kuma shawarci masu zagin nashi da cewa su gyara lamarinsu, ba'a haka.

No comments:

Post a Comment