Tuesday, 3 July 2018

Duniya ta yabawa 'yan kwallon kasar Japan saboda tsaftace filin wasa da sukayi bayan Belgium ta fitar dasu daga gasar cin kofin Duniya

Bayan kammala wasa tsakanin kasar Japan da Belgium jiya a ci gaba da buga gasar cin kofin Duniya da akeyi a kasar Rasha, sakamakon wasan ya kare Belgium na cin Japan 3-2 wanda hakan yasa Japan ta fice daga gasar, saidai duk da an fitar dasu, 'yan kwallon Japan din da magoya bayansu sunyi abin da Duniya ta yi ta yaba musu.


'Yan kwallon sun share sannan suka goge dakin da suke amfani dashi wajan canja kaya da sauran al-amuransu komai tsaf, sannan kuma suka ajiye takarda me dauke da rubutun mungode.

Kazalika 'yan wasan basu yi irin abinda wasu suke yi na kin tattaunawa da 'yan jaridu ba saboda haushin cin su da akayi, sun tsaya sun yi hira da 'yan jaridu bayan kammala wasan.

Haka kuma magoya bayan kungiyar ma sun tsince dattin dake filin kwallon bayan kammala wasan, wannan abu da sukayi ya jawo musu yabo daga sassa daban-daban na Duniya haddama daya daga cikin masu gudanarwar hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA sai da suka yabawa 'yan kwallon saboda kyakkyawar dabi'ar da suka nuna.

No comments:

Post a Comment