Friday, 13 July 2018

Fadar shugaban kasa ta baiwa Modu Sheriff shugaban kungiyar goyon bayan shugaba Buhari 2019

Kamar dai yadda Thisday da Pr Nigeria shine shugaban kasar Najeriya ya nada tsohon gwamnan jihar Borno, kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na rikon kwarya Ali Modu Sheriff a matsayin daraktan kwamitin neman goyon baya a zaben dake tafe na 2019.


Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takardar nadin da Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha ya sanya wa hannu a madadin shugaban kasar.

Shi dai wannan kwamitin ya sha ban-ban ne da Buhari Campaign Organisation (BCO) wanda a baya aka nada Ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin shugaba.

A baya dai anyi ta zargin cewa Ali Modu Sherif yana da hannu a cikin kungiyar nan ta ta'addanci ta Boko Haram.

No comments:

Post a Comment