Tuesday, 3 July 2018

Fadar Shugaban Kasa Ta Gayyato Sufeto Janar Kan Tarzoman 'Yan Sanda

Fadar Shugaban kasa ta gayyaci Shugaban Rundunar 'Yan sanda, Ibrahim Idris kan ya yi cikakken bayani game da tarzoman da wasu 'yan sanda suka yi a garin Maiduguri kan kin biyansu albashi da wasu alawus dinsu na watanni shida.


Kamfanin Dillancin Labaru na Nijeriya ya ruwaito cewa an ga Shugaban 'yan sanda a Fadar Shugaban kasa inda ya zarce kai tsaye zuwa ofishin Shugaban ma'aikatan Fadar, Abba Kyari.

Tun da farko dai, Kakakin Rundunar 'Yan sandan, Jimoh Moshood ya musanta rahotannin tarzoman  'yan sandan inda ya yi ikirarin cewa 'yan sandan sun nemi bayani ne game da albashinsu sannan daga baya suka koma bakin aikinsu.
Rariya.

No comments:

Post a Comment