Tuesday, 10 July 2018

Faransa ta fitar da Belgium daga gasar cin kofin Duniya 2018 da ci 1-0

Kasar Faransa ta fitar da Belgium daga gasar cin kofin kofin Duniya 2018 a wasan daf dana karshe da suka buga yau, wasan ya kare da sakamakon 1-0, Faransa na cin Belgium.


Dan wasan Faransa Umtiti ya ci musu kwallon da kai, baya saka wannan kwallon, musamman da wasan ya taho karewa Faransa ta koma wasan tsare gida, duk kwallon data zo ba jira ake cireta.

Mbappe ya rika faduwa akai-akai, sannan a duk sanda aka samu wani dan jinkiri 'yan wasan sun rika kokarin cin lokaci.

Shugaban kasar Faransar, Emmanuel Macron ya je kallon wasan.

Yanzu dai faransa zata jira wanda zai fito tsakanin Croatia da Ingila dan su buga wasan karshe.

No comments:

Post a Comment