Friday, 13 July 2018

FIFA ta gargadi 'yan jarida su dena yawan daukar hotunan kyawawan mata a gasar cin kofin Duniya 2018

Hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA ta gargadi 'yan jarida masu watsa yanda gasar cin kofin Duniya 2018 dake gudan a Rasha akan maida hankali da sukeyi kan kyawawan mata.


Ana zargin 'yan jarida masu daukar hotuna a gasar da maida hankali wajan yawan daukar hotuna  kyawawan mata a filayen kwallo wanda hakan yasa hukumar FIFA gargadinsu da cewa su daina.

A farkon gasar ta 2018 Rashan an yi tunanin cewa abinda zai bayar da matsala shine wariyar launin fata da kuma kin jinin 'yan Luwadi da madigo amma sai lamarin ya canja bisa yanda ake tunani, ya koma kan yin badala da mata.

Wata kungiyar kula da nuna tsangwama dake aiki da hukumar FIFA tace ta an samu matsalar tarar mata da nufin lalata a gasar ta bana kusan sau talatin, wasu lokutan an samu rahotannin sumbatar mata masu kawo rahoto da kuma taba musu jiki.

Ya kara da cewa kuma ana tsammanin lamarin zai yi kamari, kamar yanda bbcsport da irish today suka ruwaito.

Haka shima shahararren shafinnan na wallafa hotuna, watau Getty Images ya shiga wannan harkalla inda ya wallafa hotunan kyawawan mata da aka dauka a gasar ta cin kofin Duniya 2018 Amma daga baya ya ciresu ya kuma bayar da hakuri sannan ya tabbatar da cewa za'a gudanar da bincike kan hakan.

A kokarin kawo karshen wannan lamari da FIFA take yi, an sanya jami'an tsaro da su rika kula da masu irin wannan mummunar dabi'a ta neman mata da lala a gasar inda aka rika kwace takardar basu damar kallon kwallon da kuma mayar dasu kasashensu.

No comments:

Post a Comment