Sunday, 8 July 2018

Fitar da Brazil daga gasar cin kofin Duniya: Rana mafi muni a rayuwata, bani da kuzarin ci gaba da kwallo>>Neymar

Tauraron dan kwallon kafar kasar Brazil, Neymar ya bayyana fitar dasu da Belguim tayi daga gasar cin kofin Duniya da cewa itace rana mafi muni a rayuwarshi, Neymar yace abin ya bata mishi rai sosai.


Ya kara da cewa, baya tunanin zai iya samun kwarin gwiwar ci gaba da buga kwallo, amma yasan Allah zai karfafashi domin dama shine dogaronshi a dukkan abubuwan da yake yi, yace yaso su kafa tarihi amma abin takaici sai aka dakile su.

Neymar dai ya buga gasar cin kofin Duniyar 2018 inda labarin faduwarshi da juye-juye a kasa yafi kokarinshi yawa.

No comments:

Post a Comment