Sunday, 1 July 2018

Gasar cin kofin Duniya 2018: Manyan ‘Yan wasan Duniya da su ka nuna kan su

Ba bakon labari bane cewa yanzu haka dai ana can ana buga Gasar cin kofin Duniya a Kasar Rasha inda tuni aka fatattako Najeriya da duk wata Kasar Afrika tun a zagayen farko na Gasar.


Dalilin haka ne mu ka tafi Kasar Rasha domin kawowa masu karatu jerin ‘Yan wasan da ake tunani sun fi kowa kokari a Gasar. Ga dai jerin ‘Yan kwallon da tuni har sun yi zarra yanzu haka a zagayen da aka kammala:

1. Isco (Sifen)

Masana harkar kwallon kafa sun ce Isco yana cikin wadanda su ka fi kowa yin abin-a-zo-a gani a Gasar wannan karo. Isco yana cikin hatsabiban ‘Yan kwallon da su ke cin karen su babu babbaka a tsakiyar fili.

2. Philippe Coutinho (Brazil)

Dan wasan na Barcelona yana cikin masu yin abin burgewa a Gasar bana inji wadanda su ka san harkar kwallo. ‘Dan wasan tsakiyan ya zurawa Kasar sa ta Brazil kwallo kuma yana nuna kwarewar sa a wasannin su.

3. Luka Modric (Kuroshiya)

Kusan ka iya a cewa Modric na Kasar Kuroshiya shi ne wanda ya fi kowa nuna-kan-sa a Gasar na Kofin Duniya. Luka Modric dai ne ya ci Najeriya da Kasar Argetina ban da kuma irin kokarin da yake yi wa kasar sa.

No comments:

Post a Comment