Sunday, 1 July 2018

Gwamnan jihar Nasarawa ya bayar da miliyan 10 ga wadanda harin Filato ya shafa

Gwamnatin jahar Nassarawa ta bada gudunmawar kudi naira miliyan 10 ga wadanda akayi wa barna a jahar Plateau an kai harin ne a ranar Asabar inda akayi wa mutane 200 barna a wasu yankuna na Barikin Ladi dake jihar ta Plateau.


Gwamna Umaru Tanko Almakura wanda ya kai ziyarar Jaje tare da sarakunan gargajiya a gidan gwamnatin Jahar Platue sun bayyana hakan akan Wani abu da baza'a lamunta ba.

Munsan cewa wannan abu Wani nauyi ne daya rataya a wuyan jahar ta Plateau gaba daya, a matsayin mu na makotan wannan Jahar ya zama wajibi a garemu mu bada tamu gudunmawar komai kankantar ta kuwa.

Gwamna Lalong ya mika godiyar sa ga jahar Nassarawa inda yake cewa "a kowace jaha akwai mutane na kwarai da kuma akashin haka wadanda suke bada gudunmawa wajen kashe rayuka, duk wadanda suke aikata hakan suke tunanin sun tsira to basu tsiraba a wajen ubangiji, da sannu allah zai toni asirinsu."

Gwamnan ya Kara da cewa wadannan da suke tunanin sunfi karfin doka to basu fi ba ya kara da cewa " na fadawa mutanen Platue su kara hakuri su bamu hadin kai da sannu zamu bayyana wadanda sukayi wannan ta'asar.

No comments:

Post a Comment