Tuesday, 31 July 2018

Gwamnatin Buhari ta mayar da yan Najeriya tamkar mazauna gidan Yari>> Tambuwal

Alamu na cigaba da bayyana dake nuna gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ka iya ficewa daga jam’iyyar APC nan bada jimawa ba, inda aka jiyo shi yana sukar gwamnatin Buhari, wanda ya bayyanata a matsayin gwamnatin da ta mayar da yan Najeriya tamkar fursunoni.Tambuwal ya bayyana haka ne a ranar Talata, 31 ga watan Yuli, inda ya bayyana shiga sharo ba shanun da Yansanda suke yi, tare da girmankan da suke nunawa a matsayin abin Allah wadai.


“Ana danne ma yan Najeriya hakkokinsu don jin dadin wasu yan kalilan, sun mayar damu kamar wasu fursunoni mazauna gidan Yari, don haka ya zama wajibi matasa su tashi tsaye su yaki duk wani matakin dakile yancin Dimukradiyya, tare da yakar halin yunwa, rashin aikin yi, tabarbarewar kiwon lafiya, da karancin ababen cigaba da gwamnatin nan ke neman da dawwamar dasu a ciki.” Inji Tambuwal." Inji shi.

Dayake tsokaci game da hare haren da Yansanda suka kai ma shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da mataimakinsa, Sanata Ike Ekweremadu, Tambuwal yace; “Wannan abin Allah wadai ne, kuma tauye hakkin dan Adam ne, tare da cin fuska ga Dimukradiyyarmu."

Daga karshe Tambuwal ya shawarci gwamnati da cewa shi fa Dimukradiyya ya tattara ne akan bukata, kuma kowa nada yancin bin ra’ayinsa, don haka idan mutane ba zasu iya bin ra’ayinsu don bukatarsu ba, toh Dimukradiyya ba shi da amfani.

Zuwa yanzu dai gwamnan guda na jihar Benuwe ne ya fice daga APC ya koma PDP, ana sa ran gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, tare da gwamna Tambuwal zasu bi sawun takwaransu na Benuwe.

No comments:

Post a Comment