Friday, 13 July 2018

Gwamnatina na cika alkawuran da ta dauka>>Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, gwamnatinsa na cika alkawuran da ta yi wa al’ummar kasar, musamman idan aka yi la’akari da irin nasarorin da ta samu tun bayan kafuwarta.


Shugaba Buhari ya bayyana haka a yayin kaddamar da kashin farko na aikin jirgin kasan fasinja mai jigila a Abuja wato ARMTP wanda ya laukme kimanin Dala miliyan 823.5.

Buhari ya ce, kaddamar da wannan aiki, na daya daga cikin hujjojin da ke nuna cewa gwamnatinsa na cika alkawuran da ta dauka.

A cewar shugaban, gwamnatinsa ta yi bajinta a bangarorin ilimi da kuma samar da kayayyakin more rayuwa ga al’ummar kasar.

Shugaban ya bayyana kwarin guiwar cewa, wannan aikin da ya kaddamar a ranar Alhamis zai taka muhuimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin birnin tarayya Abuja.
Rfihausa.

No comments:

Post a Comment