Monday, 9 July 2018

Hakikanin Abin Da Ya Jawo Rikici Na Da Kwankwaso>>Cewar Gwamna Ganduje

Daya daga cikin manyan rikice-rikicen dake faruwa a jam'iyyar APC wanda suka ki ci suka ki cin yewa shine na tsakanin gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahu Umar Ganduje da tsohon Gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.


Rikicin tsakanin shuwagabannin yayi kamari ta yanda har Kanon ta gagari Sanata Kwankwaso shiga duk da yake cewa yana a matsayin sanata me ci.

Gwamna Ganduje ya bayyana dalilin wannan rikici nasu kamar yanda jaridar Rariya ta bayyana:

RANAR WANKA...

 “Kun taba jin muna fada a lokacin da yake (Kwankwaso) Gwamna? San-sam. Ina yi masa biyayya a matsayinsa na Gwamna kuma Ubangidana. Lokacin da Buhari ya fada mani cewa zai yi takarar Shugabancin Kasa, na fada masa cewa ni Kwankwaso zan zaba. Shugaban Kasa (Buhari) ya ji dadin yadda na bayyana masa gaskiyata ba kwane-kwane. Dukkanmu da muka je Legas sai muka zabi Kwankwaso kuma duk da cewa mun fadi zaben amma dai ba mu munafunce shi (Kwankwaso) ba. Ya kasance shugabanmu a Kano, duk da cewa talakawan Kano Buhari suka zaba, mu Kwankwaso muka zaba…

“Sai dai abin takaici, Kwankwaso ba ya kallona ko amincewa da ni a matsayin Gwamna, ya yi zaton ladabin da nake masa a matsayina na Mataimakinsa kamar ni wawa ne.

“Ka tambayi duk wanda ya san ni, ba na kaskantar da duk wani tsohon Gwamna. Dangantakata da Shekarau mai girma ce kuma mai kyau, shi ma yana daraja ni a matsayina na Gwamna. Shin mene ne yake haddasa rashin jituwa tsakanina da Kwankwaso? Matsalar ba daga gare ni ba ce ko daya, shi ne dai yake son amfani da al’ummar Kano da dukiyar Kano domin ya kalubalanci Shugaban Kasarmu da muke jam’iyya daya. Haba! Ba zan taba amincewa da haka ba, domin Buhari ya taimaka mana a lokacin da ma ba jam’iyya daya muke da shi ba. Buhari ba mamugunci ba ne, ba zai iya makirci don kaskantar da kowa, ko raba shi da mukaminsa ba. Shi ne Shugaba a yau. Da Kwankwaso ne ya ci zaben, ba zan bari Buhari ya wulakanta shi ba.

“Duk wanda ke son barin (APC), ya bari kawai. Mu yi siyasa mai tsafta, mai natsuwa…”

Fassara: Bashir Yahuza Malumfashi

No comments:

Post a Comment