Monday, 9 July 2018

Hoton ministar kudi da akawa kwaskwarim sanye da kayan bautar kasa na daukar hankula

Labarin da jaridar Premium Times ta fallasa na cewa ministar kudi Kemi Adeosun ta tsallake bautar kasa da ya kamata ace tayi bayan kammala makarantar jami'a amma sai ta yi takardar boge data nuna cewa an bata damar ba sai tayi bautar kasar ba na ci gaba da daukar hankulan mutanen kasarnan.


Wannan hoton na Ministar da akawa kwaskwarima aka saka mata kayan bautar kasar ya dauki hankula a shafukan sada zumunta inda wanda sukayi ke cewa to gashinan anganta da kaya, alamar tayi bautar kasar kenan.

Duk da cewa hoton ba da gaske bane amma ya dauki hankula sosai.

Wani abu dake kara rura wutar wannan magana shine kin fitowa tace uffan akan wannan magana da ministar tayi wanda wasu ke ganin hakan be kamata ba, ko ba dan kanta ba, dan mukamin da take rike ya kamata ta fito tayi wa jama'a bayani.

Wasu dai har sun fara kiran da'a sauke ta daga mukaminta.

No comments:

Post a Comment