Monday, 2 July 2018

Hukumar 'yansanda ta karyata cewa jami'anta sunyi zanga-zanga a Maiduguri

Hukumar 'yan sanda ta hannun babban me magana da yawunta na kasa, Jimoh Moshood ta karyata labarin cewa ajami'anta sunyi zanga-zanga yau, Litinin a birnin Maiduguri na jihar Borno bisa rashin biyansu wasu alawus-alawus da suke bi.


Sanarwar ta bayyana cewa babu wani dansanda da yayi zanga-zanga kamar yanda kafafen labarai suka ruwaito, abinda ya faru shine, wasu 'yansanda dake aiki a yankin Arewa amaso gabas sunje ofishin kwamishinan 'yansandan dake Maiduguri dan jin ba'asin tsaikon da aka samu na biyansu alawus-alawus da suke bi, amma ba ta hanyar zanga-zanga suka yi hakan ba.

Ta kara da cewa, shugaban hukumar 'yan sandan Ibrahim Idris ya baiwa kwamishinan 'yansandan umarnin gayawa 'yansandan da suka ziyarceshi dalilin rashin biyansu hakkokinsu akan lokaci da kuma tabbabatar musu da cewa tunda yanzu shugaban kasa ya sakawa kasafin kudi hannu za'a gaggauta biyansu hakkokinsu ba tare da bata lokaci ba.

Ya kara da cewa, yana kira ga jama'ar jihar Borno da su ci gaba da al-amuransu na yau da kullun ba tare da wata fargaba ba dan babu gaskiya a labarin zanga-zangar 'yansandan da ake yadawa.

Ya karkare da acewa hukumar 'yansanda hukumace me da'a da kuma sanin ya kamata ba zata saka kanta cikin abinda zai kawo tarzoma a cikin jama'a ba.

No comments:

Post a Comment