Tuesday, 10 July 2018

Idan akwai me hujjar cewa akwai Allah to ya nuna min, ni kuma nayi alkawarin sauka daga mukamina>>Inji shugaban kasar Philippines

Shugaban kasar Philippines, Rodrigo Duterte wanda shi a tsarinshi be yarda cewa akawai Allah ba, kuma yake yawan sa'in'sa da mabiya addinin kirista karkashin cocin katolica akan hakan ya kara yin wata magana da ta dauki hankulan mutane.

A baya dai shugaban ya fadi wasu kalaman batanci ga Allah.

Yanzu kuwa cewa yayi duk wanda yake da hujja ta zahiri da zata gamsar dashi cewa akwai Allah to zai ajiye mukaminshi na shugaban kasa.

Shugaban ya bayyana hakane a  gurin wani taro kan kimiyya da fasaha daya faru ranar juma'ar data gabata a birnin Davao na kasar, kamar yanda jaridar Independent ta ruwaito.

1 comment:

  1. Zai ci uban sa ku kyale shi... Ai Allah baya bukatar sai an nuna ma alamun Samuwar sa! Linpashin sa ma da kasancewar sa ai ALlah kenan ba ma sai an je nesa ba! In rokn Allah ya dauke masa gani da maga a bar shi da ji kurm, domin Allah ya nuna masa. Koda yake karamin kwaro ne shi.... Idan Allah ya so sai ya gwada masa mu'ijizar da har za ta sa ya musulinta inda kuma Allah bai yi niyyar haka kin ba sai ya bar shi cikin jahilcin sa har sai ya koma gare shi...

    ReplyDelete