Monday, 9 July 2018

Jack Wilshere ya koma West Ham United

Tsohon dan wasan Arsenal Jack Wilshere ya koma West Ham kan yarjejeniyar shekara uku, inda ya ce ya koma kulob din da ya dade yana kauna tun yana yaro.


Kwantiragin dan kwallon mai shekara 26 ta kare da Gunners a karshen watan Yuni.

"Har yanzu ina tuna lokacin da nake goyon bayan West Ham a lokacin da ina karami, na sha kallonsu a filin wasa na Upton Park," a cewarsa.

West Ham na kuma dab da kulla yarjejeniya domin sayen dan kwallon Ukraine Andriy Yarmolenko.

An fahimci cewa kudin da aka amince da Borussia Dortmund ya kai fan miliyan £17.66.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment