Thursday, 12 July 2018

Kalli abinda Mandzukic ya yiwa wani me daukar hoto wajan yin murnar kwallon da ya ci wanda daga baya dole ya dawo ya bashi hakuri

Bayan da tauraron dan kwallon kafar kasar Croatia, Mario Mandzukic yaci wa kasarshi kwallo ta biyu ana kusa da tashi, wadda ta basu nasara akan Ingila suka wuce zuwa wasan karshe, a lokacin da yake murnar cin kwallon, 'yan kasarshi sun tumurmushe wani me daukar hoto.


'Yan kwallon sun daddanne me daukar hoton ta yanda kamar dashi ke murnar cin kwallon.

Amma daga baya anga Mandzukic yazo yana bashi hakuri, rahotanni sun bayyana cewa ya ce mishi yana fatan ganinshi a wasan karshe.
No comments:

Post a Comment