Tuesday, 10 July 2018

Kalli hotunan damman harsasai da hukumar Kwastam ta kama an shigo dasu kasarnan

Hukumar hana fasa kwauri ta NCS ta yi nasarar kama wasu damman harsasai da aka shigo dasu kasarnan daga kasar Benin, yawan harsasan dai ya kai dubu dari biyu kuma wanda suka dauko su sunyi kokarin boyesu ta hanyar nuna cewa kamar jarkoki ne suke dauke dasu amma da yake dubu ta cika sai aka kama su.

Mutane biyu aka kama, direban motar, Bukari Dauda da kuma me kayan, Martin Anokwara, a jihar Naija ne aka kamasu yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Onitsha

Direban dai yace, wai shi be san meye a cikin motarba kawai dai an daukeshi aikin tuka motarne zuwa Onitsha.
No comments:

Post a Comment