Wednesday, 11 July 2018

Kalli hotunan yanda gwamna Fayose na jihar Ekiti ya fita hayyacinshi bayan da 'yan sanda suka buga mai barkonon tsohuwa

Hotunan gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose kenan lokacin da 'yan sanda suka buga mai tiyagas ya kidime, anga hadimanshi suna kokarin yayyafa mai ruwa dan ya dawo hayyacinshi, rahotanni dai sun bayyana cewa 'yan sanda sun dira a gurin da dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP ke gangamin zabe suka kama harbe-harbe.


A dalilin hakanne gwamnan da yawa mutanenshi jagora zuwa gurin taron suka hadu da jami'an 'yansanda suka harba musu barkonon tsohuwa.No comments:

Post a Comment