Monday, 2 July 2018

Kalli hotunan zanga-zangar 'yansanda yau a Maiduguri

Wadannan hotunan yanda zanga-zangar 'yan sanda ta kasance kenan a birni  Maiduguri yau, Litinin, 'yansandan na zanga-zangane dalilin rashin biyansu alawus-alawus dinsu da ba'a yi ba a kan lokaci.

Channels, Newtelegraph, bbchausa, Thisday da sauran kafafen labarai sun ruwaito cewa a lokacin zanga-zangar 'yansandan sun rika harba bindiga a iska, abinda hukumar 'yansandan ta karyata inda tace jami'an nata sunje tambayar tsaiko da aka samune na biyansu alawus-alawus dinsu cikin lumana.


No comments:

Post a Comment