Tuesday, 3 July 2018

Kamfanin NNPC Ta Bada Tallafin Naira Milyan 50 Ga Mutanen Da Ibtila'in Ruwa Da iska Ya Shafa A Jihar Bauchi

Wata babban tawaga karkashin jagorancin "lShugaban kamfanin man fetur na kasa,wato NNPC, Engr Dr  Maikanti Kachalla Baru, ta  ziyarci jihar Bauchi. Inda tawagar ta yada zangon ta a Masarautan Bauchi. Inda tawagar ta gabatar da tallafin kudi har naira milyan 50 ga mutanen da wannan ibtila'in ruwan sama da iska mai karfi a jihar bauchi ya shafa


Da yake jajantawa Mai martaba Sarkin Bauchi a fadan sa Maikanti ya ce a matsayin sa na dan jihar Bauchi ya kadu matuka da yanda Al'umma ta ta shiga wannan ibtila'in, wanda jama'a da dama suka rasa muhallin su, rayuka da kuma dukiya, 

Yace wannan jarrabawar babba ce dole ne a gare su su tallafawa jama'a  dan babu wanda ya wuci Allah ya jarrabe shi irin haka a rayuwa,

Mai martaba Sarkin Bauchi Dr Rilwanu Sulaiman Adamu CFR,  ya jinjinawa tallafin sannan yace za'a isar bisa Amana ta hanyar kwamitocin da aka kafa kan lamarin.
rariya.

No comments:

Post a Comment