Sunday, 8 July 2018

Karanta abinda Zlatan Ibrahimovic ya yi alkawarin yiwa Beckham bayanda Ingila ta lallasa Sweden a gasar cin kofin Duniya

Bayan fitar da kasarshi, Sweden daga gasar cin kofin Duniya 2018, Zlatan Ibrahimovic ya yabawa tawagar 'yan kwallon inda yace kowannensu ya cancanci a bashi kyautar kwallon zinare, yace, ba za'a taba mantawa da abinda sukayi ba har abada.Saidai kamin buga wasan su da kasar Ingila a wasan daf dana kusa dana karshe, Zlatan da David Beckham sunyi wa juna alkawarin cewa duk wanda kasarshi taci akwai abinda zai wa dan uwanshi.

Beckham yace idan Sweden taci Ingila zai kai Zlatan babban shagon nan na daya a Duniya wajan sayar da kayan katako da na dakin girki, IKEA ya saya mai duk abinda yace so.

Sannan shi kuma yana so idan Ingila ta ci Sweden, Zlatan yazo filin kwallon Wembley na Ingilar ya kuma saka rigar 'yan kwallon Ingilar su kalli wasan Ingila tare.

Wasandai ya kare da samakon Ingila na cin Sweden 2-0. Wanda hakan yasa Beckham yace to wani ya shirya zuwa Ingila.

Wayne Rooney ma ya tsokani Movic inda yace mai, yaya kake jine abokina Movic? Idan kana bukatar yin hira ka taboni.

No comments:

Post a Comment