Friday, 13 July 2018

Karanta amsar da Adam A. Zango ya bayar da wani yace mai ya rika koyi da Ali Nuhu mana

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya saka wannan hoton na mawakinnan Davido a shafinshi na sada zumunta inda yake tsakanin wasu dankara-dankaran motoci, ya kuma rubuta cewa, girma girmane kuma wanda ya fika ya fika, sai dai mai nema baya fidda rai, idan mutum ya sa Allah a gaba komai zaizo da sauki.


Har yanzu ina kan nema, kuma bazan taba karaya ba.

Bayan da Adamu ya saka wannan labari sai wani ya sokeshi da cewa, bai kamata koda yaushe ka rika saka hoton Davido a shafinka ba, saboda kaima shahararre ne, ka rika jan aji mana/sanin girman kanka mana, baka ga Ali bane?.

Adamun dai ya mayar da amsar cewa, Ra'ayin zango daban na Ali Nuhu daban kar ka dora min girman kai malam, wani jan aji, idan na fara kwambo/ kambama kaina, shi zai fara zagina. To na fada Davido ya fini suna ya fini masoya ya fini kudi kamar yadda nima nafi wasu.

Adamu ya kara cewa, wanda ya fika ya fika, ka baiwa wasu shararrun mutanen shawara(ba dai ni ba)No comments:

Post a Comment