Sunday, 1 July 2018

Karanta labarin mata masu sana'ar yin kuka a gidan mutuwa a biyasu kudi

Wani rahoto da kafar bbc yankin Afrika ta wallafa ya bayyana wasu mata 'yan kasar Ghana dake wata sana'a da ta baiwa mutane mamaki, sana'arsu itace ana daukar hayarsu a gurin da akayi mutuwa dan suyi kuka a biyasu.


Wata daga cikin masu wannan sana'a ta shaidawa bbc din cewa basu san wadanda sukewa kukan ba su dai kawai ayi tsada da sune suje suyi ta rusa kuka, ta bayyana cewa yawan kudin da suke karba ya danganta da yawan mutanen da zasu halarci gurin.

Idan mutane da yawane to za'a biya kudi da yawa idan kuma kadanne to kudin babu yawa.

Ta bayyana cewa matan dake wannan sana'a duk zawarawane da mazajensu suka mutu, sun rasa sana'ar yi shiyasa suke wannan sana'a.

Ba dai a Afrika bane kadai ake samun masu irin wannan sana'a ba, koda a shekarar da ta gabata an ruwaito wani mutum daga Arewacin Amerika, yankin Nassau na Bahamas yana tallata kanshi cewa duk me neman a mishi kuka a gurin mutuwa ya nemeshi suyi tsada yamai.

Wannan sana'a dai ta samo asaline daga kasar Masar inda ake daukar masu yin kuka da kade-kade na musamman wanda duk matane, su rika yaga kaya suna dukan jikinsu yayin da ake raka gawa kabarinta idan aka gama a biyasu.

Wannan al-ada ana kuma yinta a kasashen China da Indiya.

No comments:

Post a Comment