Tuesday, 10 July 2018

KARANTA SUNAYEN: Jam’iyyu 38 da suke dunkule wuri daya don kada Buhari

Idan dai ba a manta ba a jiya litini ne jam’iyyu 38 suka rattaba hannu a takardar amincewa suyi aiki tare don su kada Buhari a zaben 2019.


A taron da manyan ‘yan jam’iyyar PDP, APC da wasu jiga-jigan jam’iyyun hamayya duk sun rungune juna sannan sun lashi takobin ganin ko ana ha-maza-ha-mata sai sun kada Buhari da jam’iyyar sa ta APC a 2019.

Ga jam’iyyun:

AA, ADC, ADP,AGA, AGAP, APP, BNPP, C4C, DA, DPC, ACD,GPDN, GPN, Kowa party, Labour party, MAJA,MMN, MN, NCP, NGP, NUP, NIMNIP, NDCP, PANDEL, PPP, PDC, PDP,PPA,PPC, r-APC,RBNP,RPN, SDP, UPN and YDP.

Jiga-jigan ‘yan siyasar da suka halarci taron sun hada da Atiku Abubakar, Ahmed Makarfi, Ibrahim Shekarau, Sule Lamido, Okezie Ikpeazu, Dino Melaye, Gbenga Daniel da sauran su.
Premiumtimeshausa.

No comments:

Post a Comment