Sunday, 1 July 2018

Kasar Andulus ta kafa tarihin taba kwallo fiye da kowace kasa a tarihin gasar cin kofin Duniya

Duk da cewa kasar Sifaniya ta sha kashi a hannun kasar Russia wanda hakan yasa dole suka fice daga gasar cin kofin Duniyar amma sun kafa tarihin kasancewa kasar da ta fi taba kwallo fiye da kowace kasa a tarihin gasar cin kofin Duniya.

Wasan dai ya kare daci 1-1 wanda yakai ga bugun fenaret wanda ananne aka fitar da kasar.

A lokacin wasan kasar Sifaniya ta bayar da fasin dubu daya wanda babu wata kasa da ta taba yin haka a tarihin gasar cin kofin Duniya, kamin yanzu kasar Argentinace ta daya da fasin dari bakwai da uku.

Sergio Ramos kawai yayi fasin sau dari da arba'in da daya shima ba'a taba samun dan kwallon da yayi fasin masu yawan haka ba a gasar cin kofin Duniyar ba.

No comments:

Post a Comment