Tuesday, 10 July 2018

Ko da naci kofin Duniya, Ronaldo ko Messi ne za'a ba Ballon d 'Or>>Hazard

A yayin da suke shirye-shiryen buga wasan daf dan karshe, rahotanni na kara bayyana cewa, kungiyar Real Madrid na neman sayen Harzard ne idan Neymar ya kubuce mata.


Har yanzu dai Madrid na neman Neymar amma babu tabbacin zai zo kungiyar, dan hakane suka baza komarsu suna kokarin ganin idan Neymar din ya kubuce musu sai su kawo Eden Harzard.

Hazard ya gayawa BeIN Sport cewa, yana jin dadin zama a Chelsea kuma zuwa yanzu babu wata kungiya data nemi sayenshi.

Ya kara da cewa tabbas, Zidane na musammane, amma ko da Zidane ko babu Zidane Madrid kungiyace da ko wane dan kwallo ke burin buga mata wasa.

Ya kara da cewa amma fa koda Madrid din basu saye shi ba babu matsala dan yana jin dadin zamanshi a Chelsea.

Da aka tambayeshi maganar cin kofin Duniya, ya yake gani idan ya lashe kofin Duniya zai iya lashe kyautar Ballon d 'Or

Sai yace, Ronaldo ko Messi ne zasu lashe kyautar, haka bin yake koda yaushe.

Yace, na tuna wata shekara da Ribery ya cin ye duk wata gasar kwallo da ake da ita amma be samu Ballon d 'Or din ba, kamar yanda Marca ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment