Monday, 9 July 2018

Ko ruwa ko zafi muna tare da Saraki>>Kwara APC

Jam'iyyar APC reshen jihar Kwara ta ce ba za ta taba juya wa shugaban majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki baya ba.


Shugaban jam'iyyar na kwara ne Ishola Fulani ya fadi haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda yake bayyana cikakken goyon baya ga Saraki.

"Muna so mu sake jaddada cikakken goyon bayanmu ga jagorancin shugaban majalisar Dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki, komi ruwa komi zafi muna bayansa", in ji shugaban jam'iyyar ta APC a Kwara.

Ya kara da cewa: "Mun yi imanin da cewa hadin kai a APC yanzu ya yi rauni, ya tarwatse".

Wannan na zuwa bayan kotun koli ta wanke Sanata Saraki daga tuhumarsa da aka yi yin karya wajen bayyana kadarorinsa, karar da gwamnatin Buhari ta APC ta shigar a gaban kotu.

Shugaban jam'iyyar reshen Kwara, Mista Fulani ya ce, "muna farin ciki da hukuncin da ya kara tabbatar da shugaban majalisar Dattawa ba ya da wani laifi."
bbchausa

No comments:

Post a Comment