Sunday, 1 July 2018

Kofin Duniya: Faransa da Uruguay sun kori Argentina da Portugal

Uruguay
Faransa ta fitar da Argentina bayan ta doke ta 4-3, yayin da kuma Uruguay ta kora Portugal gida bayan ta doke ta 2-1 a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Rasha.


Kwallaye bakwai aka ci a wasan Kazan, inda Faransa ta doke Argentina 4-3.
Griezmann ne ya fara cin Argentina ana minti 13 da wasa a fanareti, Angel Di Maria kuma ya farke kwallon ana minti 41.
Bayan an dawo hutun rabin lokaci Mercado ya ci wa Argentina kwallo ta biyu, ana minti 48 da wasa Pavard ya farke wa Faransa kwallo a minti na 57.
Mbappé ne ya ci wa Faransa kwallaye biyu a minti na 64 da 68. Sai bayan an kara lokaci ana dab da hure wasa Agüero ya ci wa Argentina kwallo ta uku.
Yanzu an fitar da Argentina da Jamus da suka buga wasan karshe a Brazil 2014. Kuma an fitar da su ne a Kazan Arena, filin da Koriya ta kudu ta yi waje da Jamus kasar da ke rike da kofin gasar.
Hakan dai ya tabbatar da kofin duniya ya gagari Messi wanda babu abin da bai ci ba a Barcelona.
Zai iya kasancewa wannan ce gasar cin kofin duniya ta karshe ga Messi.
Da kyar Argentina ta tsallake zuwa zagaye na biyu daga rukunin D bayan ta samu sa'ar Najeriya ci 2-1.
Tun kafin haduwar Faransa da Argentina ake ganin yadda tawagar Messi ta Argentina suka sha wahala a wasannin rukuni yana da wahala su iya doke Faransa.

Uruguay ta fitar da Portugal


Ronaldo
Cristiano Ronaldo ya bi bayan Messi da aka fara kora wa gida daga Rasha.
Uruguay ta doke Portugal ne 2-1, kuma Edison Cavani ne ya ci wa Uruguay kwallayen biyu yayin da Pepe ya ramawa Portugal kwallo daya.
Cristiano Ronaldo wanda ya lashe kofin zakarun turai sau uku a jere ya kasa jagorantar Portugal ga nasarar tsallakewa zuwa zagayen kusa da dab da karshe.
Tun gasar 2006, Portugal ta kasa tsallakewa zuwa zagayen kusa da dab da karshe.
Uruguay dai tana cikin sahun kasashe uku da suka lashe dukkanin wasanninsu na rukuni, da suka hada da Croatia da kuma Belgium.
Yanzu kuma Uruguay za ta hadu ne da Faransa a zagayen kusa da dab da karshe.
Messi da Ronaldo sun lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya a shekaru 10 a tsakaninsu.
Amma yanzu wata dama ce ga sabbin jini bayan an yi waje da Messi da Ronaldo daga gasar cin kofin duniya.
rfihausa.

No comments:

Post a Comment