Sunday, 1 July 2018

Kofin Duniya: Rasha ta fitar da Spain a fanareti

Rasha ta tsallake zuwa zagayen kusa da dab da karshe bayan ta samu sa'ar Spain a bugun fanareti.


An tafi bugun fanareti ne bayan hure wasan 1-1 a minti 120 da aka shafe ana fafatawa.

Golan Rasha Igor Akinfeev ne ya kabe kwallayen Koke da Iago Aspas a bugun fanareti.

Yanzu Rasha za ta hadu ne da Denmark ko Croatia a zagayen kusa da dab da karshe.

A tarihi, Spain dai ba ta taba doke kasar da ke karbar bakuncin kofin duniya ba. Amma a wasan Spain ce ta fara zura kwallo a raga bayan dan wasan Rasha Sergei Ignashevich ya ci kansu.

A minti na 42, Artem Dzyuba ya rama wa a bugun fanareti da ta samu bayan kwallo ta taba hannun Pique.

Rasha dai ta yi kokarin rike Spain har zuwa bugun fanareti duk da cewa Spain ta fi Rasha yawan taba kwallo.

'Yan wasan Spain sun taba kwallo kusan sau hudu fiye da 'yan wasan Rasha.

Spain yanzu ta fi sahun manyan kasashen da aka fitar a gasar da suka hada da Jamus mai rike da kofin gasar da Argentina da Portugal.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment