Monday, 2 July 2018

Koriya ta Arewa na ci gaba da aiyukan makaman nukiliya cikin sirri

An bayyana cewar Amurka ta gano cewar Koriya ta Arewa a ƴan watannin da suka gabata ta ci gaba da sarrafa man makaman nukiliya a wasu yankunan kasarta a sirrince.


Wasu ma'aikatan NBC da suka nemi a sauya sunayen su sun bayyana cewar sun gano cewa a yayinda ake ci gaba da yarjejeniyar sulhu tsakanin ƙasashen Amurka da Koriya, koriyar na ci gaba da ƙera makaman nukiliya.

Baya ga man makaman nukiliya da Koriyar ke yi tana kuma ci gaba da aiyanar da harkokin makaman nukiliya a sirrince.

Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya gana da shugaban Koriya ta Arewa Kin Jong-un a Singapore a ranar 12 ga watan Yuni inda suka aminta akan warware matsalolin makaman nukiliyar Koriya ta Arewa.
Trthausa.

No comments:

Post a Comment