Wednesday, 11 July 2018

Kotu Ta Bada Umarnin Kwace Kadarorin Tsohon Gwamnan Neja

Wata Babbar kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin jihar Neja wato Minna ta amince da bukatar Hukumar EFCC na kwace wasu kadarorin tsohon Gwamnan Neja, Dakta Mu'azu Babangida Aliyu bisa zargin karkatar da wasu kudaden gwamnati.


Da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun, Mai Shari'a Yelim Bogoro ya ce, za a mikawa gwamnati kadarorin tsohon Gwamnan wadanda ke iyakacin hurumin kotun kawai na Wucin- gadi kafin a kammala shari'ar da ake yi wa tsohon na lakume Naira Bilyan biyu na kudaden canjin yanayi.

No comments:

Post a Comment