Tuesday, 3 July 2018

Kungiyar CAN ce ke ruruta wutar rikicon Benue, Filato>>Fadar shugaban kasa

Wata daga cikin masu ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin yada labarai na zamani watau Lauretta Onochie ta dura kan Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN inda tace su ke hura wutan rikicin Yankin Benuwe da Filato da sauran su a kasar.


Lauretta Onochie tayi amfani da shafin ta na Facebook tayi watsa-watsa da Kungiyar ta CAN. Onochie tace Kungiyar CAN ta Najeriya sun saki layin Ubangiji kuma babu abin da Shugabannin Kiristocin su ke yi sai yaudarar Mabiyan su da nufin tada rikicin addini a cikin kasar.

Misis Onochie wanda ta ke aiki da Shugaban kasar dai tayi dogon rubutu tana sukar Kungiyar CAN inda tace rubutun na ta bai taba sauran Kirsitoci Bayin Allah da ke kaunar Jama’a ba. Onochie tace a lokacin tsohon Shugaban kasa Jonathan, CAN ce ta zama wanda ake ba kudin sata.

Hadimar Shugaban kasar ta kuma yi tir da yadda Kiristocin Kasar su kayi shiru bayan da ‘Yan Sanda su ka damke wadanda suka kashe wani Fasto a Benuwe. Wadanda aka kama din dai duk Kiristoci ne wanda daga ciki akwai David Akenawe, Agada Tsesaa, Tarza Orvanya da Ngyohov Shin.

A rubutun da tayi dai Onochie tace ita rikakkar Kirista ce wanda ta ke aiki da littafin addinin na Kirista mai tsarki don haka ba ta aikata abin da Ubangiji ya hana. Lauretta Onochie ta koka da yadda Kungiyar CAN tayi shiru lokacin da Nnmadi Kanu da Jama’ar sa ke ta tada rikici a Najeriya.

No comments:

Post a Comment