Monday, 2 July 2018

Kwankwaso ko mazabarsa ba zai iya kawo wa ba>> Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ba zai iya lashe zabe a mazabarsa ba, ballantana ya iya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari.


Gwamna Ganduje ya fadi haka ne yayin da aka ruwaito Kwankwason na ikirarin zai iya kayar da Shugaba Buhari idan PDP ta tsayar da shi takara.

"Maganar Kwankwaso na nuna cewa ya zama rudadden dan siyasa wanda ke kama duk wata dama da ta zo masa domin ya dawo da matsayinsa a siyasance.

"Sama da shekara uku yana Majalisar Dattawa yana barci ba tare da ya gabatar da kudurin da zai amfani mutanen Najeriya ba," a cewar Ganduje, wanda tsohon na hannun damar Kwankwaso ne kafin su raba-gari.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment