Monday, 2 July 2018

Kylian Mbappe ya kafa tarihi irin na Pele da Owen a gasar cin kofin Duniya: Pelen ya tayashi murna

Matashin tauraron dan kwallon kafar kasar Faransa, Kylian Mbappe ya kamo tauraron dan kwallon kafa, Pele, a kafa tarihi bayan shekaru sittin da Plelen ya kafa nashi tarihin a gasar cin kofin Duniya.


Tun shekarar 1958, bayan da Pele ya kafa tarihin zama dan kwallo na farko me shekaru kasa da ashirin da yaci kwallaye biyu a gasar cin kofin Duniya, shekaru sittin kenan ba'a kara samun wani dan kwallo da yayi irin wannan bajinta ba sai Kylian Mpabbe.

Mbappe ya ci kwallaye biyu a ragargazar da kasarshi ta Faransa tawa kasar Argentina a wasan da suka buga na ajin kasashen 16 na gasar cin kofin Duniya 2018 da ake bugawa a kasar Rasha.

Haka kuma Mbappe ya kamo Micheal Owen da shima a shekarar 1998 ya kafa tarihin dan wasa dan kasa da shekaru ashirin da yaci kwallo daya a gasar cin kofin Duniya.

Pele ya taya Mbappe murnar wannan nasara da ya samu inda ya yi mishi fatan ci gaba da samun nasara a wasannin da kasar tashi zata buga nan gaba, amma yace banda kasar Brazil, kamar yanda ya bayyana a shafinshi na sada zumunta.

Mbappe dan shekaru 19 ya haskaka a gasar inda kuma ake tsammanin idan kasarshi takai ga wasan karshe zai iya sake kafa tarihin da Pelen ya kafa ko kumama ya zarceshi na kasancewa dan kwallo me karancin shekaru da yaci kwallo a wasan karshe na gasar cin kofin Duniya.

Lokaci dai be bar komai ba.

No comments:

Post a Comment