Tuesday, 10 July 2018

Lius Enrique ya zama sabon kocin 'yan wasan Spain

Hukumar kwallon kafa ta Spain ta bayyana tsohon kocin kungiyar Barcelona Luis Enrique a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasan kasar.


A karkashin yarjejeniyar dai Enrique zai shafe shekaru 2 nan gaba yana horar da tawagar kwallon kafar ta Spain.

A watan Yuni da ya gabata Luis Enrique ya yi murabus daga horar da kungiyar Barcelona.
Sanarwar hukumar kwallon Spain ta zabar Enrique a matsayin sabon koci, ta biyo bayan sauka daga mukaminsa da kocin ‘yan wasan kasar Fernando Hierro ya yi a jiya Lahadi, makwanni kalilan bayan da ya maye gurbin Julen Lopetegui, wanda hukumar kwallon Spain ta kora yayin da ake gaf da soma gasar cin kofin duniya.

Aikin farko da Luis Enrique zai soma da shi a matsayin na mai horar da ‘yan wasan Spain, shi ne jagorantar wasan sada zumunci da kasar za ta yi da Ingila, a filin wasa na Wembley ranar 8 ga watan Satumba mai zuwa.
rfihausa.

No comments:

Post a Comment