Tuesday, 10 July 2018

Mace mafi tsufa a nahiyar Turai ta mutu

Mace mafi tsufa a nahiyar Turai Giuseppina Projetto mai shekaru 116 ta mutu a Italiya.


Projetto ta rasu a ranar 6 ga Yuli tsakanin jama'ar Montelupo Fiorentino da ke yankin Floransa. 

Matar ta yi shekaru 116 da kwanaki 37 a duniya.

An haifi Projetto a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 1902 a tsaunin La Maddalena, a shekarun 1960 ta koma Floransa kuma ta zauna tare da danta tsawon shekaru 39 har zuwa lokacin da ta mutu.
Trthausa.

No comments:

Post a Comment