Saturday, 14 July 2018

Mai jego na shirin kafa tarihi a gasar Tennis

media
Serena Williams na gaf da kafa sabon tarihi a gasar kwallon Tennis idan ta yi nasarar lashe kofin gasar Wimbledon ta bana da ke gudana a birnin London.

A ranar Asabar mai zuwa ne Serena da ke jego, za ta fafata da Angelique Kerber ‘yar kasar Jamus a wasan karshe, watanni 10 kacal bayan haihuwa da ta yi a watan Satumba na shekarar 2017.
Idan Serena ta samu wannan nasara za ta zama mai jego ta farko da ta lashe kofi a daya daga cikin manyan wasannin kwallon tennis cikin shekaru 38, bayan tarihin da Evonne Googlagong ta kafa.
A shekarar 1980 Evonne Googlagong ‘yar kasar Australia, ta kafa tarihin zama mai jego ta farko da ta lashe kofin babbar gasar Tennis a duniya.
rfihausa.

No comments:

Post a Comment