Tuesday, 10 July 2018

Me kamfanin Facebook ya zama me kudi na 3 a Duniya

Mark Zuckerberg, yanzu shine mai kudi na uku a duniya, inda ya sha gaban Warren Buffett a jerin da jaridar Bloomberg ta rubuto na manyan masu kudin duniya.


Zuckerberg ya wuce Buffett a yayin da hannun jarin manhajar Facebook ya karu da kashi 2.4 a cikin dari, a rahoton da jaridar Bloomberg ta rawaito.

Mutum biyu da suka fi Zuckerberg a jerin sunayen sune wanda ya mallaki kamfanin nan na Amazon, Jeff Bezos da kuma shahararren attajirin nan wanda yake da kamfanin Microsoft, wato Bill Gates.

No comments:

Post a Comment