Monday, 9 July 2018

Muna da hujja akan yan siyasar dake da hannu a kashe-kashe>>Fadar shugaban kasa

A ranar Lahadi, fadar shugaban kasa tace tana dauke da hujjoji dake nuni ga cewa wasu yan siyasa ne ke da hannu a kashe-kashen da ake zargin makiyaya da aikatawa a yankunan kasar.


Ta ce wasu yan siyasa da ba’a ambaci sunayensu bane ke amfani da yan ta’adda wajen aiwatar da kashe-kashen.

Babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai da shafukan zumunta, Garba Shehu ya bayyana hakan a wata sanarwa a Abuja.

Shehu ya kara da cewa chanjin yanayi musamman bushewar tafkin Chadi, ya taimaka wajen matsalar da ake ciki.

Ya ce sauyin yanayi, wanda ya bayyana a matsayin lamari na duniya baki daya ya yi sanadiyar da yawan mutane ya karu a arewa.

Kakakin shugaban kasar ya kuma ba masu ruwa da tsaki tabbacin cewa gwamnati na cigaba da aiki don ganin ta samo mafita mai dorewa ga matsalar wacce ya bayyana a matsayin mai kunshe daa tarihi.

Shehu ya kuma roki yan Najeriya da mambobin kasa-da-kasa da su guje ma bayanan karya akan lamarin.

No comments:

Post a Comment