Wednesday, 11 July 2018

Na gaji da zaman kadaici: 'Ina bukatar matar aure'>>Inji Dangote

Attajirin dan kasuwa da yafi kowane bakar fata kudi a Duniya da Afrika gaba daya, Alhaji Aliko Dangote, wanda rahotanni suka bayyana cewa ya taba aure sau biyu yana rabuwa da matan kuma yana da 'ya'ya mata guda uku, ya bayyana cewa yana da bukatar mata.


Dangote ya bayyana hakane a wata hira da yayi da jaridar Financial Times.

Dangote yace, yanzu shekaru sun fara ja, shekara sittin ba wasa bace, yana bukatar mata, yace, (abinda yasa ya tsaya ba aure) shine ba zaka je ka auro mace ba bayan kasan cewa baka da lokacin ta, yace yanzu haka ayyuka sun mishi yawa, ga ginin matatar mai yana yi ga kamfanin taki ga aikin ajiye bututun gas, amma duk da haka zai samu ya nutsu.

Dangote kuma yayi magana akan sayen kungiyar kwallon kafa ta Arsenal inda yace yanan yana da burin sayen Arsenal inda yace yasan duka-duka ba zata wuce dala biliyan biyu ba.

Amma yanzu abinda ke ganbanshi shine kammala ginin matatar manshi amma da zarar ya gama zai mayar da hankali kan sayan Arsenal din.

Sauran abubuwan da Dangote ya bayyana a wannan hira da FT tayi dashi sun hada da cewa:

Yana Azumi, a kalla sau daya a a sati, saboda yana gyara yanayin jikin mutum.

Yana daukar kiraye-kirayen waya fiye da sau dari a kullun.

Ya kuma yi kira ga gwamnati data fito da tsarin hana shigo da Madara, Alkama da man girki daga kasashen waje.

No comments:

Post a Comment